Isa ga babban shafi
Saudiya

An fille kan wani saboda ya yi sanadin mutuwar matarsa a Saudiya

Gwamnatin Saudiya ta zartar da hukuncin kisa ga wani Mutum mai suna Fawzi al-Khaibari da aka kama da laifin ya kashe matarsa bayan ya gallaza mata azaba. Kamfanin Dillacin labaran kasar na SPA yace an fille kan Mutumin ne.

Sarki Abdallah na Saudiya
Sarki Abdallah na Saudiya AFP/Getty Images)
Talla

An zartarwa Fawzi hukuncin ne a garin Medina, wanda aka kama da laifin ya gallazawa matarsa azaba tare da kona jikinta da karfe mai wuta wanda ya yi sanadin mutuwarta.

Wannan ne kuma hukunci na farko da aka zartar a kasar Saudiya tun a ranar 8 ga watan Yuli kafin a fara Azumin Ramadana.

Alkalumman Kamfanin Dillacin Labaran Faransa sun ce jimillar mutane 58 ke nan aka zartarwa hukuncin kisa a kasar Saudiya a shekarar 2013.

Laifukan da suka shafi Fyade da kisa da Ridda da fashi da makami da safarar miyagun kwayu dukkaninsu hukuncin kisa ne ya rataya akan wadanda aka kama da aikatawa karkashin dokar Saudiya,  Hukuncin da kuma Kungiyoyin kare hakkin Bil’adama ke adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.