Isa ga babban shafi
Syria-Turkiyya

Turkiyya ta yi watsi da bukatar da Siriya ta mika mana na binciken harin bom

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya yi watsi da bukatar gwamnatin Syria na hada hannu domin binciken hare hare bom, da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 51 a karshen mako. Bayan ganawa da Shugaba Barack Obama na Amurka shugaba Erdogan na Turkiya yace gwamnatin Syria ta haramta, kamar yadda mutanen Syria suka haramta gwamnatin, yana mai cewa gwamnatin shi ba zata amince da bukatar gwamnatin Syria ba.A ranar Assabar aka kai wasu jerin hare haren bom guda biyu a Turkiya a yankin Rayhanli da ke kan iyaka da Syria.Kuma tuni Turkiya ta zargi Syria da kai harin. Amma a jiya Talata gwamnatin Syria ta bukaci makwabciyarta su hada hannu domin gudanar da binciken wadanda suka kai harin.Ministan watsa labaran Syria Omran al Zohbi yace akwai bukatar mutane Syria da Turkiya su tabbatar da gaskiyar al’amarin Kimanin ‘Yan gudun hijira 400,000 ne suka kwarara daga Syria zuwa Turkiya, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargabar rikicin Syria na iya shafar sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. 

PM kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
PM kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.