Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa da Kudu

Koriya ta Arewa ta yi wa Koriya ta kudu kashedi

Koriya ta Arewa ta aika wa Korea ta Kudu wani sabon kashedi tare da gargadin za ta dandana kudarta, muddin ba ta nuna yin nadama ba game da zanga zangar nuna kin jininta da mutanen kudu suka yi ba.

Shugabannin Koriya ta Arewa da aka cinnawa wuta a Koriya ta Kudu
Shugabannin Koriya ta Arewa da aka cinnawa wuta a Koriya ta Kudu REUTERS/Lee Jae-Won
Talla

Dubban Mutanen Kudu ne suka gudanar da zanga zangar nuna kin jinin Arewa a dai dai lokacin da Arewa ke bikin tunawa da haihuwar shugabanta na farko.

Hakan kuma bai yi ma Koriya ta Arewa dadi ba, inda ta fitar da wata sanarwa dauke da kashedin lallai sai Koriya ta Kudu ta ba da hakuri akan zanga zangar da aka yi a kasar ko kuwa ta fuskanci fushinta.

A lokcin zanga zangar, rahotanni sun bayyana cewa an ga mutanen Kudu suna kona hotunan shugabannin kasar Arewa.

A cewar hukumomin kasar ta Koriya ta Arewa idan za su mayar da martani ga makwabaciyar ba za su yi hakan da sallama ba.

Sai dai kasar Amurka, da ke goyon bayan Kudu, tuni ta yi watai da wannan barazana tana mai cewa Arewa na neman hanyar da za kwantar da barazanar da ta dade tana yi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.