Isa ga babban shafi
China

Kasar China zata kara dankon zumunci da Afruka

Sabon shugaban kasar Sin, China Xi Jinping ya bayyana kokarin da yake na kara damkon zumunci tsakanin China da kasashen nahiyar Afruka, yana mai bayyana al'ummar nahiyar Afruka a matsayin masu muhimmanci ga habakar tattalin arzikin kasar ta China. 

Sabon shugaban kasar China, Xi Jinping yana jawabi
Sabon shugaban kasar China, Xi Jinping yana jawabi 路透社
Talla

Sabon shugaban kasar China, Xi Jingping yace Nahiyar Afrika ta ‘yan Afiuka ce, dan haka ya zama wajibi ga daukacin kasashen Duniya da su mutunta Afrika su kuma dauki al’ummar yankin da darajar da Allah ya basu.

Shugaban yace a shekarar data gabata harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Nahiyar Afruka da China ta kai ta Dollar Amurka billiyan $200, kuma yace China zata kara dankon zumunci da Afrika ne, ba sassautawa zata yi ba.

Xi yace ba komai bane ga kasar ta china, ta samarwa kasashen Afrika hanyar samun lamunin kudi na Dollar Amurka billiyan 20 nan da shekaru 2 masu zuwa.

Shugaba Xi yace duk lokacin da yaje Afrika zai lura da abu biyu, dayan shine yanda ake samun cigaba a yankin, da kuma yanda al’ummar kasashen ke dada karbar kawancensu da al’mmar kasar China.

Yanzu haka dai an hakikance cewar kasar China wadda ta kasance ta biyu mafi girman tattalin arziki a Duniya, na samun albarkatun kasar da take sarrafawa ne, daga Nahiyar Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.