Isa ga babban shafi
Rasha

Shugaban China ya isa birnin Moscou domin ziyarar aiki

Sabon shugaban kasar China Xi Jinping ya isa birnin Moscou na kasar Rasha a saifiyar yau juma’a domin gudanar da ziyarar aiki a kasar, ziyarar da ita ce ta farko da ya kai a wata kasa tun bayan da aka zabe shi a kan wannan mukami a farkon wannan wata na Maris.

Shugaba Poutin na Rasha da kuma Xi Jinping na China
Shugaba Poutin na Rasha da kuma Xi Jinping na China
Talla

Jim kadan bayan saukarsa a birnin Moscou, shugaban na China ya bayyana wa manema labarai cewa, soma ziyara da kasar Rasha, na a matsayin wata alama da ke kara tabbatar da muhimmanci dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar Rasha Vladamir Poutin kuwa ya bayyana cewa, a yau dai irin alakar da ke tsakanin kasashen biyu masu karfin fada a ji a siyasar duniya ta kai wani matsayi mafi muhimmanci a cikin tarihi.
A tsawon kwanaki biyu da zai share a kasar ta Rasha, shugaba Xi Jinping da kuma takwaransa Vladamir Poutin, za su tattauna ne a game da muhimman batutuwa da suka hada da tattalin arziki da kuma fasar kimiya, sannan kuma batun man fetur da makamashi wadanda China ke bukata daga kasar Rasha.
A cikin shekaru 20 da suka gabata, an samu karuwar cinikayya a tsakanin kasashen biyu wadda ta kai ta dalar Amurka bilyan 88, kuma kasashen na fatar ganin ta kai ta dala bilyan 100 kafin karshen shekara ta 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.