Isa ga babban shafi
Tanzaniya

Shugaban China ya isa birnin Dares Salam na Tanzaniya

Sabon shugaban kasar Chana Xi Jinping a yau lahadi ya sauka a birnin Dares Salam na kasar Tanzaniya wato zango na farko na ziyarar da zai kai a wasu kasashen nahiyar Afrika da suka hada da Afrika ta Kudu da Congo Brazzaville.

Sabon shugaban kasar China, Xi Jinping
Sabon shugaban kasar China, Xi Jinping Reuters
Talla

Jirgin sabon shugaban kasar ta Chana ya sauka ne a birnin na Dar Assalam da misalin karfe 4:30 ns marece agogon GMT bayan da ya baro birnin Mosco na kasar Rasha, inda ya kai ziyarar farko a wata kasa ta ketare, tun bayan zabensa kan karagar shugabancin kasar ta Chana da Majalisar dokokin kasar ta yi a cikin wannan wata na maris.

A lokacin wannan ziyara a kasar Tanzania, shugaban na Chana zai gabatar da wani muhimmin jawabi a gobe litinin, kafin daga bisani ya sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi har guda 20 da suka shafi kasuwanci, musayar al’adu da kuma samar da ci gaba tsakanin kasarsa da Tanzaniya. Bayan ya kammala da kasar ta Tanzaniya, shugaba Xi Jinping zai wuce zuwa birnin Durban na kasar Afirka ta kudu domin halartar taron kasashen masu samun habakar tattalin arziki a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.