Isa ga babban shafi
Saudiya

Kasar Saudiyya ta fille Kan wani dan kasar Jordan akan fataucin miyagun kwayoyi

Rahotanni daga kasar Sudi Arebiya sun nuna cewar an kama Faris Salam Salama al-Maghrebi ne a lokacin da yake kokarin shiga da dimbin miyagun kwayoyin Kafso na Sinadarin amphetamine a kasar ta Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na SPA ya ruwaito.

Sarki Abdallah bin-Abdulaziz na kasar Saudi Arebiya tareda Sarkin Kuweti
Sarki Abdallah bin-Abdulaziz na kasar Saudi Arebiya tareda Sarkin Kuweti REUTERS
Talla

An dai Fille Kan Faris Salam Salam ne a Arewacin lardin Jawf na kasar ta Saudiyya.

Wannan hukuncin da aka yankewa Salam dai ya kai ga yawan wadanda aka fillewa kai 16 sakamakon safarar miyagun kwayoyi a wannan shekarar.

A shekarar 2012 kasar Saudi Arebiya ta kashe mutum 76 kamar yadda aka sama a Alkalumman gwamnati inji kamfanin dillancin labarai na AFP

Laifukan da ke janyo hukuncin kisa a kasar Saudiyya dai sun hada da Fyade, da kisan Kai, da Ridda, da fashi da Makami da safarar miyagun kwayoyi
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.