Isa ga babban shafi
Nukiliya-korea ta Arewa

Tauraron Rokan Korea ta Arewa ya samu cikas bayan harba shi samaniya

Kasar Korea ta Arewa ta tabbatar da samun cikas wajen harba tauraronta na roka a sararin samaniya wanda ya yanyo suka daga kasashen duniya wadanda suka ce shirin harba tauraron abin la’anta ne.

Wasu masu zanga-zangar kyamatar shirin Korea ta Arewa na harba Roka a samaniya inda suke kone wata tuta mai dauke da hoton shugaban kasar.
Wasu masu zanga-zangar kyamatar shirin Korea ta Arewa na harba Roka a samaniya inda suke kone wata tuta mai dauke da hoton shugaban kasar. REUTERS/Lee Jae-Won
Talla

Kasashen Duniya sun yi Allah waddai da kasar Korea ta Arewa kan kunnen uwar shegun da kasar ta yi wajen harba rokan ta sama, wanda rahotanni suka ce, harba rokan bai yi nasara ba, domin ya fada ruwa.

Kasashen Amurka, Japan da Korea ta kudu sun ce, rokan ya tashi wani lokaci kafin daga bisani ya fadi a ruwan da ke tsakanin Korea ta Arewa da Korea ta kudu.

Wannan mataki dai ya janyo mummunar suka daga kasashen duniya, yayin da ake saran kwamitin sulhu zai gudanar da taro domin tattauna batun.

Korea ta Arewa tace masanan kimiyarta na nazari kan dalilin da ya sa rokan bai yi nasara ba.

A yau Juma’a ne Korea ta Arewa ta harba tauraron a dai dai lokacin da kasar ke bukin shekaru 100 na haifuwar tsohon shugaban kasar wanda ya mutu Kim Il-Sung bayan mika ya mika mulki ga dansa Kim Jong-un.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace Shirin Korea ta Arewa abin La’anta ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.