Isa ga babban shafi

Majalisar Senegal ta amince da shirin Sall na afuwa ga 'yan adawa

‘Yan majalisar Senegal sun amince da kudirin afuwa ga fursunonin siyasar kasar wanda shugaba Macky Sall ya gabatar gabansu duk kuwa da tarnakin da ke tattare da kudirin wanda ya haddasa rarrabuwar kai a zauren Majalisar dokokin kasar.

Zaman kada kuri'a kan kudirin a zauren Majalisar Dokokin Senegal.
Zaman kada kuri'a kan kudirin a zauren Majalisar Dokokin Senegal. © Carl Klink / AFPTV / AFP
Talla

Bayan tafka doguwar muhawara ne a ranakun Talata da Laraba ‘yan majalisun 94 suka goyi bayan kudirin yayinda 49 suka kalubalance shi.

Kafin wannan muhawara dai tun a ranar Talata Majalisar ta yi watsi da kudirin wanda ta ce ba shi ne mafita ga halin da Senegal ke ciki ba.

Shugaba Macky Sall na son amfani da shirin afuwar don kwantar da hankula a rikicin siyasar da Senegal ta fada wanda zai kai ga sakin tarin fursunonin siyasar da ke tsare.

Haka zalika shirin afuwar zai kuma bayar da samar sakin hatta dubunnan magoya bayan madugun adawa Ousmane Sonko wadanda suka rika jagorantar mabanbantar bore tun faro dambarwar dan adawar da shugaba Sall. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.