Isa ga babban shafi

'Yan siyasa a Senegal sun yi watsi da gayyatar Macky Sall kan sanya ranar zabe

Mafi rinjayen 'yan takara a zaben shugaban kasar Senegal da aka jinkirta tare da wata babbar gamayyar kungiyoyin fararen hula sun yi watsi da gayyatar shugaba Macky Sall wacce za a tattauna batun ranar zabe da ya dage a farkon wannan wata.

Shugaba Macky Sall, yayin wani taron tattaunawar samun mafita kan rikicin siyasar kasar.
Shugaba Macky Sall, yayin wani taron tattaunawar samun mafita kan rikicin siyasar kasar. © Ngouda Dione / Reuters
Talla

Shugaban kasar mai barin gado Macky Sall, ya fuskanci kiraye-kirayen da ya sanya ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa bayan da ya jinkirta gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya haifar da rikicin siyasa na tsawon makonni a kasar.

Sai dai a wata hira da aka yi da shi ta wata tashar talabijin da yammacin ranar Alhamis, ya yanke shawara kan ranar har da cewa sai bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, wanda za a fara ranar Litinin.

Kazalika, ya kuma amince da ya sauka daga karagar mulki a ranar 2 ga watan Afirilu mai zuwa, sai dai ya ce dole ne a samu wanda zai gajeshi kafin gudanar da zaben kasar.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.