Isa ga babban shafi

Alaka na kara tsami tsakanin Benin da Nijar

Dangantaka tsakanin Nijar da makwabciyarta Benin na dada yin tsami la’akari da cewar a baya-bayan nan hukumomin kasar ta Benin suka dau matakin yin gwanjon wasu kayayyakin ‘yan kasuwar Nijar da ke tashar ruwan Cotonou.

Tun bayan juyin mulkin Nijar ne dangantakar kasashen biyu ke kara tsanani
Tun bayan juyin mulkin Nijar ne dangantakar kasashen biyu ke kara tsanani AFP - PROSPER DAGNITCHE
Talla

 

Yayin da wasu shugabannin ‘yan kasuwar ke ganin hakan ba zai yiwu ba, wasu kira suka yi ga hukumomin kasashen biyu su tattauna da juna domin samun mafita.

A jumlace dai kwantenonin ‘yan kasuwar na Nijar dubu 13 da 600 ne ke jibge a tashar ruwan ta Cotonou tsawon watanni kafin al’amurra su tsananta biyo bayan takunkumin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa Kasar sakamakon juyin mulki.

Amma  daga bisani hukumomin mulkin sojin kasar ta Nijar sun dauki gabarar taimaka wa yan kasuwar domin fito da kayayyakin ta kasar Togo.

To sai dai kasancewar wasu daga cikin wadannan kayayyakin na can ne tun shekarar 2021, akwai wadanda suka wuce wa’adin da ya kamata su yi a tashar ruwan.

Dalilin da yasa hukumomin kasar ta Benin suka dauki matakin yin gwanjon Kwantainonin kusan  800.

Lamarin da shugaban kungiyar yan kasuwa masu shigowa da fitar da kayayyaki daga kasar ta Nijar Alhaji Sani Shekarau ya ce ba za ta sabu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.