Isa ga babban shafi

'Yan ciranin Senegal 24 sun mutu bayan nutsewar jirginsu a Teku

Mahukuntan Senegal sun tabbatar da tsamo gawarwakin akalla ‘yan cirani 24 wadanda jirgin da ke dauke da su ya nutse a arewacin kasar jiya Laraba, ‘yan ciranin da ke kan hanyarsu ta fara balaguro zuwa nahiyar ta Turai ta tekun Atlantic.

Ko a bara 'yan cirani fiye da dubu 6 da 600 suka mutu a tekun na Atlantic a kokarinsu na tsallakawa Turai.
Ko a bara 'yan cirani fiye da dubu 6 da 600 suka mutu a tekun na Atlantic a kokarinsu na tsallakawa Turai. AFP - HANDOUT
Talla

Gwamnatin lardin Saint Louis, Alioune Badara Samb da ke tabbatar da faruwar hadarin ya ce zuwa yanzu, anyi nasarar tsamo mutane 21 da ransu baya ga gawarwaki 24, duk da cewa bai bayar da alkaluman yawan mutanen da ke cikin jirgin ba.

Wasu ganau sun shaidawa AFP cewa adadin ‘yan ciranin da jirgin ke dauke da su ya zarta 300 lamarin da ke nuna ana ci gaba da laluben akalla mutum 250 a cikin ruwan wanda ke matsayin gabar tekun Atlantic.

A cewar Samb da dama daga cikin wadanda hadarin jirgin ya rutsa da su sun yi iyo zuwa gabar ruwa tare da bazuwa cikin kananun kauyukan da ke gefen gabar ruwan dalilin da zai bayar da matukar wahala a iya tantance adadin mutanen da jirgin ke dauke da su.

Tashar jiragen ruwan jihar ta Saint Louis mai yawan tabo, na matsayin hanya ga tarin ‘yan ciranin Senegal dama na kasashen makwabta da ke kwarara zuwa Turai lura da yadda ta hade da tekun Atlantic.

Mamady Dianfo guda cikin wadanda suka tsira da ransu a hadarin ya ce adadin fasinjan ya kai 300 yayinda Alpha Balde shi ma wani fasinja na daban ke cewa adadin ya haura 200.

Ko a bara akalla ‘yan cirani dubu 6 da 600 suka mutua kan hanyarsu ta zuwa Spain ta hanyar amfani da tekun na Atlantic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.