Isa ga babban shafi

'Yan ciranin yammacin Afrika dubu 7 sun tsallaka Spain cikin wata guda

Ma’aikatar harkokin wajen Spain ta bayyana karuwar adadin ‘yan ciranin Afrika da ke tsallakawa tsibirin Canary ta hanyar amfani da kananun jiragen ruwan ta tekun Mediterranean da fiye da kashi dubu guda idan an kwatanta da alkaluman wadanda suka tsallaka a shekarar da ta gabata.

'Yan ciranin na ci gaba da bin hanyoyin masu matukar hadari a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai.
'Yan ciranin na ci gaba da bin hanyoyin masu matukar hadari a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai. AP - Cecilia Fabiano
Talla

Alkaluman da ma’aikatar cikin gidan Spain ta fitar a yau Juma’a na nuna yadda ‘yan ciranin yammacin Afrika dubu 7 da 270 suka isa kananun tsibiran da ke tekun Atlantic daga ranar 1 zuwa 31 ga watan Janairu wanda ke nuna kusan ninki 13 na adadin da suka isa a makamancin lokacin cikin shekarar da ta gabata na mutum 566.

Yankin na kan tekun Atlatic mai dauke da kananun tsibirai da ake kira Archipelago na matsayin matattarar masu yawon bude idanu a Spain, inda ko a bara sai da ‘yan ciranin yammacin Afrika dubu 39 da 910 suka shiga Turai ta hanyar amfani da mashigin.

Alkaluman ma’aikatar ya nuna cewa tsibirin El Hierro da ke jerin kananun tsibiran na Spain ya karbi bakin hauren da yawansu ya ninka adadin al’ummar yankin na mutum dubu 9 a shekarar 2023.

Rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Walking Borders ta fitar, ta sanya safarar ta tekun Atlantic zuwa tsibirin na Canary a matsayin balaguro mafi tattare da hadari wanda ‘yan ciranin kan dauki kasada wanda bayanan ke nuna yadda hanyar ta lakume rayukan mutum dubu 6 da 7 a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.