Isa ga babban shafi

Hanyar Libya zuwa turai na ci gaba da lakume rayukan 'yan Afirka

Sannu a hankali hanyar kustsawa Libya zuwa turai na ci gaba da zama mai hadari, inda har wasu ke yi mata lakabi da hanyar kiyama, la’akari da yadda mutanen ke mutuwa kowacce rana, amma duk da haka ana samun karuwar masu sha’awar bin ta zuwa Spaniya ko kuma Italiya.

Har yanzu akwai miliyoyin 'yan Africa da ke sha'awar wannan tafiya
Har yanzu akwai miliyoyin 'yan Africa da ke sha'awar wannan tafiya AFP - BEN STANSALL
Talla

Hanyar na cikin fitattun hanyoyin da ‘yan Africa ke bi wajen tsallakewa zuwa turai, yayin da wasu ke bata bat, a tsakiyar teku.

Masu irin wannan tafiya kan dauki kasadar amfani da kananan jiragen ruwa da nufin tsallakawa, ba tare da kayan kariya ba.

Ko a farkon makon nan, irin haka ta faru, inda jirgi guda dauke da bakin hauren ya yi batan dabo kan tekun Mediterranean.

To sai dai kuma a yau mahukunta sun sanar da gano jirgin da ke dauke da mutane 126, kuma kafatanin su basu da cikakkiyar lafiya, inda wasu ke fama da karancin ruwa a jikin su, tsantsar gajiya da kuma cututtukan da ake kamuwa da su sanadin tsananin sanyi.

Wani karamin jirgin ruwan masu yunkurin tsallakewa zuwa turai
Wani karamin jirgin ruwan masu yunkurin tsallakewa zuwa turai AFP - SAMEER AL-DOUMY

Wannan na faruwa ne a dai-dai lokacin da ake da banbancin yanayi sossai tsakanin kasashen gabashin Africa da ke fama da tsananin zafi yanzu haka da kuma nahiyar turai da ake zubar da ruwan kankara.

Bayanai sun ce kusan dukannin wadanda aka ceto din sun saddakar cewa mutuwa zasu yi, sakamakon halin tashin hankalin da suka shiga.

Cikin wadanda aka ceto din akwai jariri sabuwar haihuwa guda 1, sai kananan yara 30 wadanda suka dauki aniyar wannan tafiya mai hadari ba tare da wani babba da zai kula da su ba.

Mutanen da ake ceto sun shaidawa mahukunta cewa sun taso ne daga iyakar Libya kwanaki 4 da suka gabata sai dai kuma igiyar teku ta kada karamin jirgin nasu zuwa wani bangaren da ya juyarwa da direban kai, dalili kenan da ya sa suka rika walagigi a tsakiyar ruwa

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.