Isa ga babban shafi

Fiye da 'yan cirani dubu 6 sun mutu a kokarin tsallakawa Spain ta ruwa a 2023

Akalla ‘yan cirani dubu 6 da 618 suka rasa rayukansu cikin shekarar da ta gabata a kokarinsu na tsallakawa Spain ta ruwa, adadin da ke nuna mutuwar mutum 18 a kowacce rana.

'Yan cirani na ci gaba da mutuwa a kowacce rana a kan hanyarsu ta ratsa tekun Mediterranean don samun rayuwa mai inganci a Turai.
'Yan cirani na ci gaba da mutuwa a kowacce rana a kan hanyarsu ta ratsa tekun Mediterranean don samun rayuwa mai inganci a Turai. © Cecilia Fabiano / AP
Talla

Kungiyar da ke kare hakkin ‘yan cirani ta Spain, alkaluman ‘yan ciranin da suka mutu a 2023 ya ninka sau 3 idan an kwatanta da alkaluman wadanda suka mutu a shekarar 2022 na mutum dubu 2 da 390, lamarin da ta kira da mai matukar tayar da hankali.

A cewar Helena Maleno babbar mai kula da shirye-shiryen kungiyar ta Walking Borders yayin jawabinta gaban taron manema labarai ta ce alkaluman shi ke matsayin adadi mafi yawa tun bayan faro ayyukanta a shekarar 2007.

Ms Helena ta ce adadin  na mutum dubu 6 da 618 ya kunshi kananan yara 384 wadanda ko dai suka mutu ko kuma suka bace a hanyar ta shiga Spain daga tekun Mediterranean.

Alkaluman Walking Borders sun nuna cewa a duk mace-mace da kuma bacewar da ta faru akan hanyar ta shiga Spain galibi ya fi faruwa a gabar ta Atlantic da ke ratsa tsibirin Canary daga matafiyan da ke ratsowa ta Afrika inda mutane dubu 6 da 7 suka mutu a baran.

Bayan tsaurara matakan shige-da-fice ta ruwa tsakanin kasashen da ke da gaba ta tekun na Mediterranean, hanya daya ta iya isa ga Turai ita ce ta tsibirin na Canary wadda galibin masu son tserewa yunwa ko tashe-tashen hankula daga Afrika ke amfani da ita.

Kungiyar ta koka da yadda ‘yan ciranin ke kama hanyar tafiyan ba tare da isasshen abinci ko ruwan sha ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.