Isa ga babban shafi

'Yan ciranin Tunisia 40 sun yi batan dabo a tekun Mediterranean

Akalla ‘yan ciranin Tunisia 40 ne suka yi batan dabo akan tekun Mediterranean bayan kama hanyar shiga Turai ta gabar ruwan kasar kamar yada majiyoyi suka tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Dubunnan 'yan cirani ne ke ci gaba da bacewa a tsakar tekun na Mediterranean a hanyarsu ta zuwa Turai.
Dubunnan 'yan cirani ne ke ci gaba da bacewa a tsakar tekun na Mediterranean a hanyarsu ta zuwa Turai. AFP - SAMEER AL-DOUMY
Talla

Jami’an tsraon gabar teku a Tunisia a jiya Talata sun tabbatar  da bacewar ‘yan ciranin akan hanyarsu ta zuwa Italiya cikin makon jiya.

Jami’an tsaron sun bayyana cewa tun bayan daina jin amon bakin hauren su fiye da 40 ne aka shiga lalubensu sakamakon gaza isarsu Italiya kamar yadda suka nufa, amma har zuwa yanzu ba a kai ga gano su ba.

Wasu faifan bidiyo sun nuna yadda jami’an tsaron gabar tekun da taimakon jiragen shalkwafta ke ci gaba da shawagi a kan tekun a kokarin gano inda ‘yan ciranin suka shige.

Yanzu haka dai Tunisia ita ta maye gurbin Libya wajen kasancewa matattara ko kuma tashar tarin ‘yan ciranin da ke kokarin shiga Turai daga Afrika.

Galibi ‘yan ciranin Afrika da ke kokarin tserewa talauci don samun rayuwa mai inganci a Turai na amfani da gabar ruwan ta Tunisia don isa nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.