Isa ga babban shafi
Najeriya

Fusatattun matasa sun auka wa motoci dauke da buhunnan abinci a Neja

Jami’an sojoji sun tarwatsa fusatattun matasa da suka auka wa wata mota dauke da kayan abinci a jihar Neja ta Najeriya.

Matsalar na kara zafafa a Najeriya, lamarin da ke haifar da zanga-zanga
Matsalar na kara zafafa a Najeriya, lamarin da ke haifar da zanga-zanga The Guardian Nigeria
Talla

Bayanai sun ce jami’an sojojin sun yi ta harbin bindiga a sama don tarwatsa mutanen da suka tare motocin dakon abincin da ke kan hanyar su ta zuwa Abuja daga Kaduna.

Wasu ganau da suka tattauna da manema labarai sun ce mutanen sun sace buhunnan shinkafa da yawa daga cikin motocin da suka aukawa, kafin zuwa jami’an tsaro.

Wannan dai ya sake fito da matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa da jama’ar kasar ke fama da ita.

Matakin na zuwa ne dai-dai lokacin da aka sami rarrabuwar kawuna a tsakanin kungiyoyin kwadago na kasar da suka sanya ranar 26 ga watan da muke ciki na Fabariru don gudanar da zanga-zanga.

To sai dai a yau kungiyar TUC ta sanar da janye gudanar da zanga-zangar, inda ita kuma kungiyar NLC ta dage kan cewa zata gudanar da zanga-zangar ba gudu ba já baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.