Ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso na iya rura wutar matsalolin yankin - Masana
Kwararru sun yi gargadin cewa barazanar da ake fuskanta saboda matakin Nijar, Mali da Burkina Faso na daura aniyar ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS ka iya zarta yadda ake tunani.
Wallafawa ranar:
Masanan sun ce muddin aka gaza warware matsalar ta fuskar tattaunawa, to fa baya ga matsalar tsaro, ficewar kasashen uku daga ECOWAS, ka iya rusa hada-hadar kasuwancin kusan dala miliyan 150 da ke gudana duk shekara a tsakanin kasashen yammmacin Afirka.
Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin siyasar kasa da kasa a Najeriya da ke Jami’ar Bayero a Kano, ya tabbatar wa sashin Hausa na RFI cewar, babu kuskure a gargadin kwararrun, la’akari da yanayin da yankin yammacin Afirka ke ciki.
Farfesa Kamilu Sani Fagge kan aniyar Mali da Burkina Faso da Nijar ta neman ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS
Yanzu haka dai akwai batutuwa da dama da suka jefa miliyoyin mutane ‘yan kasashen kungiyar ta ECOWAS mai manbobi 15 cikin zurfin tunani, musamman kan yadda makomarsu za ta kaya idan har lamurra suka rincabe kamar yadda ake fargaba.
Daga cikin muhimman batutuwan da makomarsu ke daukar hankali dai akwai matsayin miliyoyin mutanen da ke zaune a kasashe makwaftansu da ke yammacin nahiyar ta Afirka, albarkacin cewa babu bukatar takardun biza da kuma bai wa mutane damar samun guraben aiki a kasashen da ba nasu ba, a tsakanin manbobin kungiyar ECOWAS.
Ga misali, wata kididdiga ta nuna cewar a Ivory Coast kadai, akwai ‘yan kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar sama da miliyan 5 wadanda ke aiki.
A bangaren makwaftaka kuwa, Nijar na da iyakar da tsawonta ya kai akalla kilomita dubu 1,500 tsakaninta da Najeriya.
Sai kuma bangaren kasuwanci inda kashi 80 cikin 100 na hada-hadar kasuwancin da al’ummar Nijar ke yi na gudana ne tsakaninsu da Najeriya, alkaluman da Abba Sadik shugaban wata cibiyar bincike mai suna CIRES da ke birnin Paris ya tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu