Isa ga babban shafi

Kasashen Mali da Burkina Faso sun mika wa ECOWAS wasikar ficewa a hukumance

Kasashen Mali da Burkina Faso sun mikawa ECOWAS takardar bukatar ficewarsu daga kungiyar a hukumance, a wani yanayi da ake kyautata zaton Nijar ta bi bayansu kowanne lokaci daga yanzu.

Wani zaman taron ECOWAS.
Wani zaman taron ECOWAS. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

A Lahadin da ta gabata ne gwamnatocin kasashen Mali Nijar da Burkina Faso suka sanar da ficewa daga cikin kungiyar ta kasashen yammacin Afrika, bayan da suka zargi kungiyar da yi musu barazana.

Sai dai tun a wancan lokaci ECOWAS ta bayyana cewa ta na dakon wasikun kasashen 3 a hukumance kan bukatar ficewa daga kungiyar.

A cewar ECOWAS yanzu haka ta na aiki tukuru wajen samar da maslaha a kasashen 3 wadanda dukkaninsu ke karkashin mulkin Soji.

Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta aikewa da AFP kwafin wasikar ficewar yayinda Burkina Faso ta shaidawa kamfanin dillancin labaran aikewa da ta ta wasikar.

Babu dai cikakken bayani daga Nijar, sai dai wasikun kasashen biyu sun fayyace dalili iri guda a matsayin hujjar da ta tunzura su ficewa daga kungiyar.

Karkashin dokokin ECOWAS dai ana bukatar akalla shekara guda wajen aiwatar da wasu shirye-shirye ga duk kasar da ke son ficewa daga cikin kungiyar.

Kasashen na Mali da Burkina Faso da kuma Nijar na matsayin mambobin da aka kafa kungiyar ta ECOWAS da su tun a shekarar 1975 sai dai a baya-bayan nan suna fuskantar takun saka bayan juyin mulkin da Soji a kasashen wanda ya kai ga kakaba musu takunkumai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.