Isa ga babban shafi

ECOWAS ta bayyana dalilin soke tattaunawar da ta shirya da gwamnatin sojin Nijar

Kungiyar kasashen yammacin nahiyar Afrika ECOWAS ko CEDEAO ta ce ta soke tattaunawar da ta shirya yi da jagororin Mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ne biyo bayan matsalar da jirgin saman da ta yi hayarsa ya samu a rana juma’a.

Shugabannin kasashen kungiyar  ECOWAS/CEDEAO a taron kungiyar na 64 a birnin Abidjan na Ivory Coast a ranar 10 ga watan Disamba 2023.
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO a taron kungiyar na 64 a birnin Abidjan na Ivory Coast a ranar 10 ga watan Disamba 2023. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

A wata sanarwa, ECOWAS ta ce tawagarta da za ta yi wannan tattaunawa ta shafe lokaci mai tsawo a filin tashi da saukar jiragen sama na Abidjan a kasar Ivory Coast sakamakon wannan matsalar da jirgin ya samu, tana mai cewa za ta tsaida wata rana a nan gaba kadan don tataunawar.

 

Kungiyar ta kasashen Yammacin Nahiyar Afrika ta kakaba wa Nijar takunkuman karayar tattalin arziki masu tsauri ne biyo bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed da sojoji suka yi a watan Yulin shekarar da ta gabata, amma yanzu tana kokarin ganin an samar da dimakardiyyar a kasar ta hanyar tattaunawa.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa zababen shugaban Jamahuriyar Nijar, Bazoum ne dangantaka ta yi tsami tsakanin sojojin da ECOWAS ko CEDEAO, biyo bayan barazanar fito-na-fito da ta yi da masu juyin mulkin.

Masana na ganin tattaunawa ta diflomasiyya ce kawai za ta kai ga cimma masalaha a wannan rikici da ya kunno kai tun a watan Yulin shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.