Isa ga babban shafi

Benin ta sanar da shirin dawo da alaka tsakaninta da Nijar bayan juyin mulki

Shugaba Patrice Talon na Benin ya bayyana cewa lokaci ya yi da yakamata alaka ta dawo tsakanin kasar da makwabtanta da ke karkashin mulkin Soji, bayan juyin mulkin da ya haddasa musu takunkumai tsaurara daga manyan kasashe da kungiyoyi.

Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyyar Benin.
Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyyar Benin. AFP - ERIC PIERMONT
Talla

A jawabinsa na shekara shekara ga ‘yan kasa gaban majalisar tarayyar kasar, shugaba Talon ya ce akwai lokacin da ya kamata ayi ala wadai akwai kuma lokacin da za a mika bukatu haka zalika akwai lokacin taka-tsan-tsan a cikin nazari a alakar da ke tsakanin Nijar da Benin.  

Talon wanda kalaman na sa kai tsaye ke nufin halin da ake ciki a alakar kasar da makwabciyarta Nijar tun bayan hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamad a watan Yulin da ya gabata, ya shaidawa zaman majalisar cewa akwai bukatar sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su yi abin da ya dace wajen bayyana hakikanin manufarsu da kuma abin da suke bukata daga kasashen duniya.

A cewar shugaban na Jamhuriyyar Benin dabara ta rage ga gwamnatin Sojin Nijar wanda ya zama wajibi su tsarkake niyyarsu wajen tafiyar da kasar mai fama da takunkuman kasashen duniya.

Takunkuman da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta kakaba kan Nijar tun bayan juyin mulkin da ya kai ga kulle iyakoki ciki har da wadda ta hada kasar ta Benin, kai tsaye ya gurgunta tattalin arzikin kasar ta yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.