Isa ga babban shafi

Nijar ta kaddamar da bututun man da ta shimfida zuwa Benin

Shugabannin sojojin da suka karbi mulki a Nijar sun kaddamar da wani katafaren bututun mai da zai kai danyen mai zuwa makwabciyar kasar Benin domin isar da shi zuwa kuma kasuwar duniya.

Ma'aikata daga Nijar da kuma China, yayin da suke rangadin aikin bututun mai a yankin Gaya, ranar 10 ga watan Oktoba, 2022.
Ma'aikata daga Nijar da kuma China, yayin da suke rangadin aikin bututun mai a yankin Gaya, ranar 10 ga watan Oktoba, 2022. AFP - BOUREIMA HAMA
Talla

An ce bututun man mai tsawon kusan kilomita 2,000 zai baiwa Nijar damar sayar da shi a kasuwannin duniya ta tashar ruwan Seme da ke Benin.

An gudanar da bikin kaddamar da aikin a yankin Agadem mai nisan sama da kilomita 1,700 daga Yamai babban birnin kasar.

Firaminista Ali Zeine ya bayyana cewa za a yi amfani da albarkatun da ake amfani da su don tabbatar da 'yancin kai da ci gaban kasar.

An rufe iyakar Nijar da Benin ne biyo bayan kakaba takunkumi mai tsanani da kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta kakaba mata bayan kwace ikon da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli.

Ministocin makamashi na kasashen Mali da Burkina Faso, wadanda suka nuna goyon baya ga sabbin shugabannin Nijar kuma dukkansu sun yi juyin mulkin soja ne a cikin shekaru biyu da suka gabata, sun halarci wannan gagarumin bikin.

Ya kamata dai a kammala aikin bututun a cikin shekarar 2022 amma yaduwar cutar Covid-19 ta jinkirta shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.