Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane sama da 20 a Afrika ta Kudu

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 21 a garin Ladysmith dake lardin KwaZulu-Natal na kasar Africa ta kudu.

Ambaliyar ta yi munin da har yanzu ba'a kai ga gano wasu gawarwakin ba
Ambaliyar ta yi munin da har yanzu ba'a kai ga gano wasu gawarwakin ba REUTERS - STRINGER
Talla

Da yake bayani kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Kanal Robert Netchiunda ya ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 21 kuma akwai fargabar adadin ka iya karuwa saboda yawan mutanen da suka bata.

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta fara ne ranar kirismeti, kuma kawo yanzu ta rushe gidaje fiye da 1,400.

A karin bayanin da ya yi, jami’in dan sanda Netshiunda ya ce har yanzu akwai masu aikin ceto cikin ruwan da ya shafe yankin don ganin ko za’a zakulo karin gawarwaki, kuma za’a ci gaba da aikin neman har zuwa safiyar gobe litinin.

Guda daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya shaidawa manema labarai cewa iyalan gidan sa 7 ne suka rasa rayukan su lokacin da ruwan ya tafi da motar da suke ciki ya kuma jefa ta cikin kogi a ranar ta kirismeti.

Sai dai ya ce jami’an sun yi nasarar tsamo kanin sa da matarsa da kuma ‘ya’yan sa guda 4 dan uwan sa  da kuma dan yayan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.