Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 30 a yankin Igabi ta jihar Kaduna a Najeriya

'Yan bindiga a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya sun shiga kauyen Unguwar Liman da ke yankin Gwada cikin karamar hukumar Igabi, inda su ka yi awon gaba da  mutane talatin da daya kafin daga bisani mutum uku su ka kubuta daga hannun su.

Har yanzu ba'a ji wani bayani daga wadanda aka yi garkuwa da su ba
Har yanzu ba'a ji wani bayani daga wadanda aka yi garkuwa da su ba © dailypost
Talla

Malam Abdulrahman Mohammed mazaunin garin ne ya kuma shedawa RFI HAUSA cewa a cikin wadanda akayi garkuwa da su har da matar dan uwansa da kuma ‘ya’yanta.

Ya kuma ce har yanzu 'yan bindigar ba su kira su ba domin jin halin da 'yan uwansu ke ciki.

" Yan bindigar sun shigo da misalin sha biyu na dare kuma su ka dinga harbe-harbe kafin daga bisani su kutsa cikin wasu gidaje inda suka kwashi mutum talatin da daya cikin harda jarirai suka wuce amma daga baya mutum uku sun dawo gida," a  cewarsa".

Sai dai har  ya zuwa yanzu jami'an tsaro ba su ce komai dangane da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.