Isa ga babban shafi
AUREN JINSI

Uganda ta yi tir da takunkuman rashin adalci da Amurka ta sakamata kan ta haramta auren jinsi

Kasar Uganda ta yi kakkausar suka ga kasar  Amurka bisa fadada takunkumin hana shiga jami'anta a kasar, inda ta fassara hakan a matsayin wani yunƙuri  na halasta wa  kungiyar ‘yan madigo da luwadi  ta LGBT bisa manufar kasar ta Uganda na yakar masu auren jinsi.

wani hoto na yan auren jinsi a Ouganda
wani hoto na yan auren jinsi a Ouganda AP
Talla

Wadannan sabbin takunkuman da aka bayyana a farkon wannan makon sun shafi mutanen Uganda ne, wadanda ba a tantance su a hukumance ba. A cewar Amurka, su ne ke da alhakin rasa kawo cikas ga mulkin dimokuradiyya da murkushe kungiyoyin, gami da ‘yan kunguyar LGBTQ masu madigo.

Henry Okello Oryem, karamin ministan harkokin wajen kasar, ya dage da cewa kasarsa ba za ta ja da baya kan   kudirin ta ba.

Ya shaida wa AFP cewa babu shakka game da gaskiyar cewa wasu kungiyoyi a Amurka da kuma na Yamma suna neman kawo yan Afirka da Uganda don karbar dangantaka ta jima'i ta hanyar amfani da taimako da lamuni" a matsayin riba.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya yi tambaya: Me ya sa ba za su kakaba wa kasashen Gabas ta Tsakiya takunkumi iri daya ba, wadanda ke da irin wadannan dokoki ko kuma masu tsauri kan 'yan LGBT?

Yace, Idan suka hana 'yan majalisarmu bizar za su je Shanghai, Guangzhou. Akwai kyawawan wurare da yawa da za mu ziyarta.

Amurka ta aiwatar da wani mataki na farko na takunkumin shiga jami'an Uganda a watan Yuni, a matsayin martani ga dokar hana luwadi da madigo ta Uganda.

Bayan takunkumin na Amurka, Bankin Duniya ya kuma dakatar da sabon ba da lamuni ga Uganda a watan Agusta.

Dokar ta tanadi hukunci mai tsanani ga mutanen da ke da alaka da luwadi da kuma inganta luwadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.