Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da tsare Bobi Wine a gida bayan ya koma Uganda daga Afirka ta Kudu

Jagoran 'yan adawar kasar Uganda Bobi Wine ya ce wasu 'yan bindiga ne suka kama shi tare da tsare shi a gidasa lokacin da ya dawo daga kasar Afirka ta Kudu.

Madugun 'yan adawar Uganda, tsohon mawaki Robert Kyagulanyi, da aka fi sani da Bobi Wine.
Madugun 'yan adawar Uganda, tsohon mawaki Robert Kyagulanyi, da aka fi sani da Bobi Wine. AFP
Talla

Mawakin wanda ya rikide ya zama dan siyasa, shi ne babban mai kalubalantar shugaba Yoweri Museveni, wanda ya shafe kusan shekaru 40 yana mulkin kasar.

An kama matashin mai shekaru 41 a lokuta da dama kuma ya fuskanci tuhume-tuhume da dama ciki har da cin amanar kasa.

'Yan sanda sun musanta kama Bobi Wine, suna masu cewa an raka shi gida ne kawai domin bashi cikakken tsaro.

Bobi Wine, wani tsohon fitaccen mawaki ne, wanda sunansa na gaskiya Robert Kyagulanyi, ya yi yunkurin neman shugabancin kasar a zaben da aka yi mai zafi tsakaninsa da shugaba Museveni mai shekaru 79 a shekarar 2021.

A gangamin yakin neman zabensa tare da wasu 'yan adawa an kashe akalla mutane 54 bayan na bayyana taron da sunan zanga-zangar kin jinin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.