'Yan sandan Uganda sun dakile wani harin bam na kungiyar ADF
'Yan sandan Uganda sun dakile wani harin bam da kungiyar 'yan tawaye ta ADF ta kai a yau Lahadi mai tazarar kilomita 50 daga Kampala babban birnin kasar. Shugaban kasar Yoweri Museveni da kan sa ne ya sanar da wannan gaggarumar nasar da yan Sanda suka samu,inda ya karasa da cewa rahotanni da binciken sa sun tabbatar da cewa kungiyar ta ADF shirya bama-bamai biyu, wadanda "suna shirin dasa su a cikin majami'u a Kibibi, da Butambala".
Wallafawa ranar:
Shugaban da ya rubuta hakan a shafinsa na X, tsohon Twitter, ya yaba da kokarin jami’an tsaro da suka samu korewa da karin kayan aiki suka kuma samu nasarar kwance wadanan bama-bamai.
A watan Satumba, 'yan sandan Uganda sun ce sun dakile wani harin bam da aka kai a babban cocin Kampala, inda suka kama wani mutum da ake zargi da kokarin tada bam a tsakanin masu ibada.
A watan Yuni, 'yan bindigar ADF sun kashe mutane 42 ciki har da dalibai 37 a wata makarantar sakandare da ke yammacin Uganda kusa da kan iyaka da DR Congo. Wannan dai shi ne daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai a kasar Uganda tun bayan harin biyu da aka kai a birnin Kampala a shekara ta 2010 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 76 a wani samame da kungiyar al-Shabaab ta Somaliya ta dauki alhakin kaiwa.
A cikin rahotonsa na baya-bayan nan a cikin watan Yuni, wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya tabbatar da cewa kungiyar ISIS na daga cikin masu baiwa kungiyar ADF tallafin kudi tun a kalla 2019.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu