Isa ga babban shafi

Dokar kisa kan masu auren jinsi za ta fara aiki kan wani matashi a Uganda

Wani matashi mai shekaru 20 ya zama mutum na farko da mahukuntan Uganda suka samu da laifin neman jinsi, wanda ke nuna zai fara fuskantar tuhuma kuma matukar aka same shi da laifi, kai tsaye za a yanke masa hukuncin kisa, kamar yadda sabuwar dokar haramta auren jinsi daya ta kasar ta tanada. 

Wani matashi da ke fafutukar tabbatar da 'yancin masu auren jinsi a Uganda.
Wani matashi da ke fafutukar tabbatar da 'yancin masu auren jinsi a Uganda. AP - Rebecca Vassie
Talla

Duk da matsin lambar da Uganda ta fuskanta daga kasashen yammaci da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama, hakan bai hana ta samar da dokar ba a watan Mayun da ya gabata. 

A cewar wasu bayanai da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya samu, sun nuna cewar wanda ake zargi an shigar da kararsa ne a ranar 18 ga wannan watan, bayan da ya aikata laifin da ake zargin sa da wani mai shekaru 41. 

Daraktar Yada Labarai a ofishin mai gabatar da kara na kasar Jacqueline Okui, ta tabbatar da gurfanar da matashin a gaban wata kotun majistare a ranar 18 ga wannan wata, inda kotun ta bada umarnin tsare shi. 

Lauyan wanda ake tuhuma Justine Balya, ta bayyana cewa tuhumar da ake yi wa matashin ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar, inda ta tabbatar da wanda take karewa ne ya zamo mutum na farko da aka fara tuhuma da laifin neman jinsi daya a kasar, sai dai ba ta yi karin harske a kan hakan ba. 

Duk da cewa Uganda ta kwashe shekaru ba tare da ta zartar da hukuncin kisa ba, amma akwai dokar da ta tanadi hakan, inda ma a ka ji shugaban kasar Yoweri Museveni a shekarar 2018 na cewa, za a dawo da zartas da hukuncin kisa don rage aikata laifuka a sassan kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.