Sama da mutum miliyan biyu ne ke fama da lalurar kwakwalwa a Ghana - WHO
Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar, ya ce akwai mutane fiye da milyan 2 da dubu 400 da ke fama da lalurar tabin hankali a kasar Ghana kawai.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:11
Rahoton ya ce wannan matsala na kara ta’azzara saboda karancin jami’n kiwon lafiyar da ke da kwarewa a wannan kula da masu tabin hankali a kasar.
A watan Fabrairu ne, kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta shawarci gwamnatin Ghana da ta kawo karshen irin yadda ake tsare da mutane masu tabin hankali a kasar.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Abdallah Sham’un Bako.
A yayin taron kungiyar da aka yi a shekarar 2017, gwamnatin Ghana ta goyi bayan shawarwari 10 cikin 11 da suka shafi 'yancin masu bukata ta musamman, ciki har da hana, cin zarafin bil'adama asibitocin kula da masu lalurar kwakwalwa.
A cikin Nuwamban 2022, Human Rights Watch ta gano fiye da mutane 60, ciki har da wasu yara, daure cikin sarka, da kuma wadanda aka killace a cikin keji yayin da ake azabtar da su da yunwa da kuma rashin tsaftar muhallin da aka ajiye su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu