Isa ga babban shafi

Mutanen da harin ADF a makaranatar Uganda ya kashe ya haura 40

Hukumomin Uganda suka ce adadin wadanda mayakan ADF masu alaka da kungiyar IS suka kashe bayan harin da suka kai wata makarantar sakandaren kwana a kan iyakarsu da jamhuriyar demokradiyar Congo ya kai 41, galibinsu dalibai, wanda ke zama hari mafi muni da kasar ta gani cikin sama da shekaru goma.

Harabar makarantar sakandaren da mayakan ADF suka kai wa hari a Uganda. 16/06/23.
Harabar makarantar sakandaren da mayakan ADF suka kai wa hari a Uganda. 16/06/23. AP - Hajarah Nalwadda
Talla

Rundunar sojin Uganda ta ce tana bin diddigin maharan na kungiyar ‘yan tawayen ADF, wadanda suka yi garkuwa da mutane shida a lokacin harin da suka kai makarantar da yammacin Juma’a, kafin su arce Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Jami’ai da shaidu sun ce an yi amfani da bindigogi da wukake yayin mummunan harin da aka kai cikin dare tare da kona dakunan kwanan dalibai a makarantar sakandare ta Lhubiriha da ke Mpondwe.

Jami'an 'yan sanda da sojoji sun zargi kungiyar ADF, daya daga cikin mayaka da suka fi muni a kan iyakar gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wanda kungiyar IS ta ce reshen ta ne.

Sylvester Mapozi, magajin garin Mpondwe-Lhubiriha inda aka kai harin, ya ce an kashe dalibai 39 a makarantar.

Da yawa daga cikin wadanda suka mutu sun kone ba a iya gane su ba, yayin da har yanzu ba a kai ga gano wasu daliban ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.