Isa ga babban shafi

Daliban da suka mutu a harin mayakan ADF a wata makarantar Uganda sun kai 37

Sanarwar baya-bayan nan da rundunar sojin Uganda ta fitar ta ce dalibai 37 da suka hada da da kananan yara ne suka mutu a wani harin ta'addanci da kungiyar ADF mai alaka da IS ta kai wata makaranta a yammacin Uganda cikin dare.

Wasu mayakan ADF a ƙauyen Manzalaho kusa da Beni a watan Fabrairu 2020.
Wasu mayakan ADF a ƙauyen Manzalaho kusa da Beni a watan Fabrairu 2020. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Da fari dai kakakin 'yan sandan Uganda Fred Enanga ya ce ADF da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ta kai hari a wata makarantar sakandare a Mpundwe cikin daren Juma'a inda suka kona wani dakin kwanan dalibai da kuma sace kayan abinci, bayan kashe mutane 25.

Ya ce, ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane 25 daga makarantar kuma an kai su asibitin Bwera da ke kusa da iyakarsu da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Kazalika wasu dalibai takwas da suka samu raunuka cikin mawuyacin hali na asibitin Bwera suna samun kulawar gaggawa.

Gandun dajin Virunga

Enanga ya ce dakarun soji da na 'yan sanda sun bi maharan da suka gudu zuwa gandun dajin Virunga da ke kan iyaka da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Makarantar bata wuce kilomita biyu daga kan iyaka da Jamhuriyar Demokradiyar Congo.

Bacewar wasu dalibai

Shugaban gundumar Joe Walusimbi ya shaidawa AFP cewa har yanzu ba’a kai ga tantance adadin dalibai da suka ba ce ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.