Isa ga babban shafi

An binne mutane 33 da suka rasa rayyukan su bayan harin Kaduna

Akalla mutane 33 ne aka binne sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Runji da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.Duk da cewa an shirya yin hakan, har yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba ta bayar da cikakken bayani kan adadin wadanda suka mutu a harin ba.

Daya daga cikin unguwani a jihar Kaduna
Daya daga cikin unguwani a jihar Kaduna AFP PHOTO / MICHAEL SMITH
Talla

Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harakokin cikin gida na jihar, ya ce sojoji sun sanar da gwamnati harin wanda ya faru a daren asabar.

Gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu tare da yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.

Mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa an binne mutane 33 bayan harin. Sun ce wasu da dama sun samu raunuka.

Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kaduna.
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kaduna. © Wikimedia Commons

John Hayab, Darakta Janar na Gidauniyar Zaman Lafiya ta Duniya, ya zargi jami’an tsaro a wannan fanni da mayar da hankali kan karbar cin hanci da rashawa a wajen masu ababen hawa, maimakon kare lafiyar mazauna yankin.

John  Hayab ya ce masu kisan sun mamaye al’ummar ne suna kashe mutane ba tare da kakkautawa ba bayan da suka ba mazauna yankin sanarwar cewa za su zo su lalata da kashe mutane a cikin al’umma.

Ya ce baya ga wadanda aka kashe, an kona sama da gidaje hudu.

Ya koka da yadda ake samun rashin tattara bayanan sirri daga hukumomin tsaro.

Harin na ranar asabar da wasu ‘yan bingiga da ba na jihar suka kai shi ne na biyu cikin mako guda.

Shugaban kungiyar ci gaban al’umma ta Atyap, wata kungiya mai zaman kanta a yankin, Sam Timbuwak, ya ce kisan na farko ya faru ne a ranar Alhamis a al’ummar Atak’Njei.

Ya ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne daga wani daji da ke kusa da wurin inda suka fara harbin bindiga, inda suka kashe mutane takwas a cikin lamarin.

Zangon Kataf da ke Kudancin Kaduna na daya daga cikin wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula da wasu ‘yan bangar jihar ke yi.

Har ila yau, a yankuna da dama na jihar, 'yan ta'adda suna kashewa, da raunata su tare da yin garkuwa da mutanen domin neman kudin fansa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.