Isa ga babban shafi

Uba Sani ya zama zababben gwamnan jihar Kaduna

Bayan shafe sa’o’i da dama ana jiran sanin sakamakon kuri’un da aka kada a zaben kujerar gwamnan Kaduna, hukumar zabe ta bayyana Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda yayi nasara.

Zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani na jam'iyyyar APC tare da magoya bayansa.
Zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani na jam'iyyyar APC tare da magoya bayansa. © Twitter/@ubasanius
Talla

Yayin sanar da sakamakon, babban jami’in hukumar INEC na jihar ta Kaduna kuma mataimakin shugaban jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis, ya ce Uba Sani ya samu kuri'u 730,002 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Isa Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 719,196.

Ita kuwa jam’iyyar Labour wadda Jonathan Asake ya  tsaya mata takara a zaben gwamnan na Kaduna, kuri'u 58,283 ta samu, yayin da dan takarar jam'iyyar NNPP, Suleiman Hunkuyi ya samu kuri'u 21,405.

Kafin sanar da sakamakon zaben na Kaduna dai, Danjuma Sarki, wakilin jam’iyyar PDP da ke zauren da ake tattara alkaluman, ya ki amincewa da adadin kuri’un da aka ce sun samu, inda ya ce sahihin lissafin da suka bibiya sau da kafa ya nuna cewar sun samu kuri’u 713,157 ne, yayin da APC ta samu 709,561.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.