Isa ga babban shafi
Mali

MDD za ta sanya takunkumai ga Kungiyar 'yan tawaye a Mali

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kungiyar ‘yan tawayen kasar Mali, ta fara neman hanyoyin da za a kulla yarjejeniyar zaman lafiya yayin da Majalisar ta ce, a shirye take ta kakaba takunkumi kan duk kungiyar da bata ajiye makamai ba  

'Yan tawayen Abizinawa
'Yan tawayen Abizinawa
Talla

Mambobin Kwamitin tsaron na MDD , sun ce, yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a ranar 1 ga watan Maris wata dama ce mai cike da tarihi, da za a samar da zaman lafiya a kasar Mali.

Kungoyoyi da kasashen duniya da dama, suna ta kokarin ganin an samar da zaman lafiya a kasar Mali, dake gab da durkushewa tun bayan da mayaka masu kishin Islama suka karbe arewacinta a shekarar 2012.

A wata Sanarwar da kwamitin tsaron ya fitar, ya nemi babbar gamaiyyar ‘yan tawayen Abizinawa da ake kira Coordination, su fara nemo hanyoyin da za kulla yarjejeniyar.

A ranar Alhamis, Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya nemi kwamitin da ya kara matsin lamba ga kungiyar Coordination, ta amince da yarjejeniyar.

Ministan ya kuma ce, rugujewar yarjejeniyar zaman lafiyan da aka kulla a baya, babbar barazana ce ga kasar Mali, da ma yankin yammacin Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.