Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

An kubutar da wani dan Nedelan da ke hannu kungiyar Aqmi a Mali

A samame da suka kai a yankin arewacin kasar Mali, dakarun sojan kasar Fransa sun kubutar da wani dan kasar Nedelan da kungiyar Aqmi mai alaka da alka’ida a yankin sahel ta yi garkuwa dashi tun cikin 2011

Dakarun Faransa
Dakarun Faransa
Talla

Dan kasar Nedland din da aka yi garkuwa da shi Mr Sjaak Rijke, an sace shine tun a ranar 25 novembre 2011 a garin Tombouctou dake arewacin kasar ta Mali, ya kuma samu kubuta ne a yau litanin a karkashin wani samamen da dakarun sojan kasar Fransa dake kasar Mali suka kaddamar

Ma’aikatar ministan tsaron kasar Fransa ta ce dakarun sojan na Fransar sun kama mutane da dama daga cikin mayakan na al’ka’ida

Yanzu haka dai bature da aka kubutar an isar da shi wani wajen mai cikkaken tsaro a garin Tessalit, inda sansanin wucin gadin rundunar yaki da yan ta’adda a yankin Sahel ta Barkhane yake.

Ma’aikatar tsaron  Fransa ta kara tabbatar da cewa Mr Rijke,na cikin koshin lafiya

A lokacin da ya ziyarci tsakkiyar kasar Fransa a yau litanin domin halartar tunawa da zagayowar ranar da 'yan sandan kasar Jamus suka harbe wasu yaran yahudawa 44 yau shekaru 71 da suka gabata

Shugaban kasar Fransa Francois Hollande ya shidawa manema labarai cewa, dakarun na Fransa basu da masaniya da kasancewar Baturen a inda suka kai samamen katari aka yi ya samu kubuta

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.