Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Ziyarar Kerry a Najeriya

Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry ya ce gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da kuma lokacin da aka shirya zaben, abu ne mai matukar muhimmaci a Najeriya, a yayin da kasar ke fuskantar barazanar Mayakan Boko Haram da ke da’awar kafa daula.

Sakataren Harakokin Wajen Amurka john Kerry yana ganawa da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kuma Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar PDP
Sakataren Harakokin Wajen Amurka john Kerry yana ganawa da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kuma Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar PDP Reuters
Talla

Kerry ya kawo ziyara a Najeriya a karshen mako inda ya gana da Dan takarar Jam’iyyar adawa ta APC Tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da kuma Shugaba mai ci Goodluck Jonathan da ke neman wa'adi na biyu.

Kerry ya ce hankalin duniya yanzu ya karkata a Najeriya domin ganin an gudanar da karbabben zabe cikin kwanciyar hankali.

Sannan ya ce Amurka a shirye ta ke ta bai wa Najeriya tallafi don yaki da ta’addanci da taimakawa, wajen ganin kasar ta gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

 Kerry ya gana da Buhari tare Goodluck Kuma bayan kammala ganawar ya shaidawa manema labarai a birnin Lagos cewa kasashen duniya suna bin yadda al’amurran siyasa ke tafiya a Najeriya sau da kafa.

Sakataren Harakokin Wajen Amurka john Kerry yana ganawa da Janar Muhammadu Buhari Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar adawa ta APC
Sakataren Harakokin Wajen Amurka john Kerry yana ganawa da Janar Muhammadu Buhari Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar adawa ta APC Reuters

Mr Kerry ya ce zaben nagari ne kawai zai taimaka wajen yaki da ayyukan ‘yan bindiga, domin Shugaba Barack Obama ne ya turo shi don tattaunawa da masu ruwa da tsaki ga sha’anin siyasa a Najeriya.

Ya kuma ce ya gana da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya ba shi tabbacin gudanar da sahihin zabe a Najeriya.

Wannan kuma ake ganin zai kawo karshen cece-kucen da aka fara yi a kasar kan yiwuwar dage zabukan na wata mai zuwa.

Rikicin Boko Haram shi ne dai muhimmin abu da ya dami kasashen duniya.

Tun 2009, Sama da mutane 13,000 Boko Haram ta kashe tare da tursasawa mutane sama da miliyan gujewa gidajensu.

Yanzu haka kuma Mayakan Boko Haram sun kwace garuruwa da dama a Jahohin da ke arewa maso gabacin Najeriya.

Wannan ne kuma babban kalubalen da ke gaban gwamnatin Goodluck Jonathan wanda masu fashin bakin ke ganin shi zai yi sanadin faduwarsa a zaben 14 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.