Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta zabi Buhari a matsayin Dan takara

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben fitar da gwani na Jam'iyyar adawa ta APC bayan ya samu rinjayen kuri'u 3430 fiye da sauran 'Yan takara guda hudu da ke neman zama 'Yan takarar Jam'iyyar a zaben 2015. Buhari ya ba Alhaji Atiku Abubakar tazarar Kuri'iu fiye da 2400.

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari Reuters
Talla

Wakilan Jam’iyyar kusan 800 ne suka jefa kuri’ar zaben Dan takarar shugaban kasa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya samu Kuri'u 954.

Buhari ya ba Alhaji Atiku Abubakar tazarar Kuri'iu fiye da 2400, yayin da ake ci gaba da kidaya kuri’un akwatin Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso.

'Yan takara guda biyar ne suka fafata a Zaben na babbar Jam'iyyar APC a Najeriya, Tsohon Shugaban kasa Janar Buhari  da Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Imo Rochas Okorocha da Mawallafin Jaridar Leadership Sam Nda Isaiah.

Sai dai Kwankwaso na yi wa Atiku barazana da yawan kuri’u.

Yanzu dai Buhari zai sake tunkarar Jam'iyyar PDP mai mulki bayan ya dade yana fafatawa da 'Jam'iyyar a zabukan da suka gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.