Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP da APC za su tabbatar da ‘Yan takara

Manyan Jam’iyyun siyasar Najeriya za su gudanar da manyan tarukansu na Kasa domin tabbatar da ‘Yan takarar shugaban kasa a zaben 2015. Jam’iyyar PDP mai mulki zata tabbatar da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takararta yayin da APC mai adawa zata zabi Dan takara daga cikin mutane biyar.

Tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar 'Yan takarar Jam'iyyar adawa ta APC
Tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar 'Yan takarar Jam'iyyar adawa ta APC
Talla

PDP mai mulki zata gudanar da taronta ne a birnin Tarayya Abuja domin tabbatar Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takara bayan wanda ya bayyana aniyarsa ta yin tazarce.

Tuni Gwamnonin Jam’iyyar da Kwamitin amintattun Jam’iyar PDP suka amince da Goodluck Jonathan a matsayin dan takara tilo.

Jam’iyyar APC mai adawa kuma zata gudanar da babban taronta ne a birnin Lagos da ke kuduncin kasar, inda wakilai kimanin 8,000 za su zabi daya daga cikin ‘yan takara 5 da ke neman wakilatar Jam’iyyar a zaben shugaban kasa.

‘Yan takarar sun hada da tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Imo Rochas Okorocha da kuma Sam Ndah Isaiah mawallafin jaridar Leadership.

Duk dai wanda APC ta tsayar shi zai fafata da Shugaba Goodluck Jonathan a zaben 2015 da masu fashin baki suke ganin shi ne mafi zafi a tarihin siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.