Isa ga babban shafi
Ebola

Yaduwar Ebola daga Dabba zuwa mutum ta fi hanzari inji Masana

Masu bincike sun gano cewar fiye da mutane miliyan 22 a Nahiyar Afruka ne ke zaune a wuraren da Cutar Ebola ke iya yaduwa daga Dabbobi zuwa mutane, abinda suka bayyana a matsayin babban abin kulawa

Duas parteiras, usando material para proteção contra o ebola, entregam um recém-nascido para a mãe na Libéria.
Duas parteiras, usando material para proteção contra o ebola, entregam um recém-nascido para a mãe na Libéria. UNFPA Libéria
Talla

Duka-duka dai inji shi wannan Rahoton mutane miliyan 22 da doriya ne ke zaune a wurare masu matukar hatsari da kuma Cutar ta Ebola ke yaduwa daga Dabbobi zuwa mutane a kasashe 22 na Nahiyar Afruka.

Kuma inji Rahoton, mutane miliyan 21 da doriya kwatankwacin kashi 97 na zaune ne a yankunan karkara.

Barkewar Cutar Ebola ta baya-bayan wacce kuma ta fi kamari cikin shekaru 40 inji Rahoton ta kashe akalla mutane 2,000 daga cikin 4,000 da suka kamu da ita a yankin yammacin Nahiyar Afruka daga watan Disamban Bara zuwa 31 ga watan Agustan Bana.

An kuma samu barkewar Cutar ne a kasar Guinea, inda daga nan ne ta yadu zuwa kasashen Liberia da Sierra Leone da kuma tarayyar Najeriya, kuma yanzu haka Cutar sai dada karuwa take.

Kwararrun dai basu maida hankali ga yanda Cutar ke yaduwa daga mutum zuwa mutum ba, amma sun lissafa sakamakon bincike da ya nuna yanda aka samu yaduwar cutar har sau 30 daga Dabbobi zuwa mutane.

Wannan kuma ya faru ne kama daga shekarra 1976, kamin daga bisani, a samu barkewar cutar ga mutane 2,322 daga kasar Zaire.

Yanzu dai a yankin gabashin Afruka Najeriya ce kan gaba, a yayin da kasar Mozambique ke a yankin Kudanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.