Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun karbe ikon garin Ashigashya

‘Yan Sanda a kasar Kamaru sun ce yayan kungiyar Boko Haram sun kwace garin Ashigashya na Najeriya da ke kan iyakar kasashen biyu bayan sojojin Najeriya sun tsallaka zuwa cikin Kamaru. Kakakin ‘Yan Sandan Kamaru ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mayakan sun shiga garin a ranar Litinin tare da yanka mutane uku

Abubakar Shekau Shugaban Kungiyar Boko Haram.
Abubakar Shekau Shugaban Kungiyar Boko Haram. (Boko Haram/AFP)
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Boko Haram ya yi ikirarin kafa daular Musulunci a garin Gwoza da suka kwace iko a cikin wani sakon bidiyo.

Rahotanni sun ce daruruwan mutanen Ashagashya ne suka tsallaka zuwa kamaru domin samun mafaka bayan Mayakan na Boko Haram sun abkawa garin.

Wani Mazauni garin Mubi a Jihar Adamawa ya tabbatarwa RFI Hausa cewa Sojojin Najeriya da suka tsallaka kasar Kamaru wadanda ma’aikatar tsaron kasar tace sun yi shi ne a matsayin dabarun yaki sun dawo garin na Mubi.

Bayan tserewar Sojojojin zuwa Kamaru, Rahotanni sun ce Mayakan Boko Haram sun kuma karbe ikon Gamboru Ngala tare da karbe ofishin ‘Yan sanda da barikin Sojoji a garin.

Yanzu haka dai Mayakan na Boko Haram suna rike da ikon garuruwan Buni Yadi na Jihar Yobe da Gwoza da Gamboru Ngala da kuma Ashigashya da suka kwace a Jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.