Jonathan ya nada Shekarau Ministan Ilimi
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada wasu sabbin Ministoci guda hudu da suka hada da Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da Stephen Oru da Adedayo Adeyeye da Abdul Bulama, bayan Majalisa ta tantance su.
Wallafawa ranar:
Jonathan ya nada Shekarau a matsayin Ministan Ilimi, Adeyeye karamin Ministan ayyuka, Oru a matsayin Ministan yankin Niger Delta sai Bulama a matsayin Ministan Kimiya da Fasaha.
Ana dai ganin wannan wasu matakai ne da shugaban na Najeriya ya dauka domin gina wadanda zasu yi masa yakin neman zaben shugaban kasa wa’adi na biyu, kodayake bai fito yace zai sake yin takara ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu