Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan zai yi yaki da ta’addanci don kare dimokuradiya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha alwasin yaki da ta’addanci domin kare demokuradiya da aka kwashe shekaru goma sha biyar kasar na cin moriya. Shugaban ya fadi haka ne a cikin jawabinsa ga ‘Yan kasa a ranar bikin dimokuradiya.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da uwargidansa Patience a ziyarar da suka kai a Afrika ta kudu
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da uwargidansa Patience a ziyarar da suka kai a Afrika ta kudu Reuters
Talla

Shugaban yace hadin kan kasa da dorewar mulkin demokuradiya na fuskanta barazana daga hare haren ta’addanci.

Shekaru 15 ke nan da Najeriya ta dawo mulkin demokuradiya daga mulkin Soji, amma yanzu an kwashe shekaru sama da biyar kasar na fama da tabarbarewar tsaro inda dubban mutane suka mutu.

Batun sace ‘Yan matan Chibok sama da 200 kuma ya ja hankalin duniya, inda yanzu manyan kasashen irin su Amurka da Faransa da Birtaniya suka aiko da kwararru domin kokarin kubutar da  ‘Yan matan da mayakan Boko Haram suka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.