ECOWAS
ECOWAS ta kira taron gaggawa akan Mali da Najeriya
Kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta kira wani taron gaggawa na Shugabannin kasashen kungiyar domin tattauna matsalar tsaro musamman a Mali da Najeriya. Shugabannin zasu tattauna game da barazanar hare haren ta’addanci a yankin da ke fitowa daga Mayakan Boko Haram, kamar yadda Kakakin shugaban kasar Ghana ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa.
Wallafawa ranar:
Talla
Ben Malor ya kuma ce a ranar Juma’a ne za’a gudanar da taron wanda zai kuma tattauna halin da ake ciki a kasar Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu