Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Za a dakatar da tallafin abibci da ake baiwa kasar Zimbabwe

Kusan al’ummar kasar Zimbabwe miliyon daya, na fuskantar bala’in yunwa, bayan da kwamitin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, yace zai dakatar da baiwa kasar tallafin abincin da aka saba bayarwa. Kwamitin ya dauki wannan matakin ne, sakamakon rashin kudun ci gaba da baiwa kasar tallafin da aka saba bayarwa.Mai Magana da yawun kwamitin abincin na MDD a kasar ta Zimbabwe Tomson Phiri, yace sun zafatre tallafin abincin da suke baiwa mutane miliyonn daya a kasar kuma ba mamaki a kara ragewa a nan gaba.Alhaji Isa Tafida Mafindi, mashahurin manomi ne a nahiyar Africa, ya ce korar manoma turawa da aka yi daga kasar ta Zimbabwe, ya sa ‘yan kasar da basa amfani da kayan aikin zamani, basa iya noma isashshen abincin da ake bukata a kasar.Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace tana bukatar kudaden da suka kai dalar Amurka Miliyon 80, don ciyar da ‘yan kasar da ke da bukata, a cikin watannin 6 masu zuwa.Buhari Bello Jega mai sharhi ne kan siyasar Nahiyar Africa, yace takun saka da hukumomin kasar Zimbabwe ke yi da kasashen yamma, na daga cikin abubuwan da suka sa aka dakatar da tallafin.An kiyasta cewa a kalla mutane Miliyon da dubu 200, ko kuma rubu’in al’ummar kasar da ke zaune a yankunan karkara ne za su bukaci tallafi abinci, nan da watan Mayu, lokacin da za a yi girbin amfanin gona.Kuma tuni farashin kayan abinbci ya yi tashin gwaron zabo a kasar ta Zimbabwe. 

Wata mace tana noma a Zimbabwe
Wata mace tana noma a Zimbabwe
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.