Isa ga babban shafi
Mogadishu

Kungiyar al Shabaab ta kaddamar da yaki a Moghadishu

Kungiyar Al Shabaab a kasar Somalia, ta kaddamar da sabbin hare hare a birnin Moghadishu, a kokarin da take na kifar da Gwamnatin kasar, da kuma kwace iko. Bayan an kwashe sama da sa’oi 24 ana bata kashi, tsakanin dakarun kungiyar da kuma dakarun samar da zaman lafiya, na kungiyar kasashen Afrika, bayanai sun ce mutane kusan 60 sun rasa rayukansu, cikinsu harda Yan Majalisu 11, yayin da kusan 100 suk asamu raunuka.Wani jami’in tsaro yace, kungiyar Al Shabaab ta kai hari wani otel a Moghadishu, inda jami’an Gwamnati ke zama, inda suka bude masa wuta, kuma sukakashe mutane da dama, cikinsu harda Yan Majalisun kasar.Daga bangaren Gwamnati, an bada sanarwar kashe Yan kungiyar Al Shabaab 15.Kanar Mohammed Omar, babban jami’in tsaron Gwamnatin Somalia, ya tabbatar da barkewar sabon fada yau da safe, a Yankunan Holwadag, Hodan, da kuma Bondhere. 

Kakaaki kungiyar Al Shabaab
Kakaaki kungiyar Al Shabaab
Talla

Kungiyar Al Shabaab a kasar Somalia
Kungiyar Al Shabaab a kasar Somalia Reuters

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.