Isa ga babban shafi
Bangladesh

An yanke wa Nizami na Jam’iyyar Musulmi hukuncin kisa

Kotun kasar Bangladesh ta yanke wa shugaban Jam’iyyar Jama’atul Islam hukuncin Kisa bayan samunsa da aikata laifukan yaki a shekara ta 1971 lokacin da kasar ke yakin samun ‘yancin kai daga Pakistan.

Motiur Rahman Nizami, Shugaban Jam'iyyar Jama'atul Islam da aka yanke wa hukuncin kisa a Bangladesh
Motiur Rahman Nizami, Shugaban Jam'iyyar Jama'atul Islam da aka yanke wa hukuncin kisa a Bangladesh PHOTO/AFP
Talla

Kotun ta samu Motiur Rahman Nizami da aikata laifuka 71 da suka hada da kisa da fyade da kuma wawurar dukiyoyin jama’a lokacin yakin samun ‘yanci.

Tuni dai Hukumomin Kasar Bangladesh suka tsaurara matakan tsaro a cikin kasar saboda yiyuwar barkewar rikici daga magoya bayan Jam’iyyar idan aka yanke hukuncin a shari’ar da ake yi wa shugaban Jam’iyar Jama’atul Islam, babban Jam’iyyar Musulunci a kasar.

Irin wannan hukuncin da aka yanke wa wasu mataimakan Nizami sun haifar da tashin hankali a cikin kasar wanda ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 500.

Ministan cikin gida Asaduzzaman Khan yace sun dauki duk matakan da suka dace don dakile duk wani tashin hankali a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.