Isa ga babban shafi

Masu Korona za su iya shiga gasar Australian Open

Daraktan shirya gasar kwallon Tennis ta Australian Open, Craig Tiley, ya ce ba za su bukaci 'yan wasa su yi gwajin cutar COVID-19 ba a gasar ta bana, kuma za ma su iya fafata wasan, ko da kuwa suna dauke da kwayar cutar.

Rafael Nadal na kasar Spain bayan lashe kofin gasar Australian Open ta shekarar 2022
Rafael Nadal na kasar Spain bayan lashe kofin gasar Australian Open ta shekarar 2022 AP - Andy Brownbill
Talla

Sauyin da aka samu, wanda Tiley ya ce na da nasaba da irin matakan sassautawa ko janye dokokin takaita walwala saboda Korona da ake yi a garuruwan da ke makwaftaka da Melbourne, da sauran sassan duniya.

Gasar Australian Open ta shekarar 2021 ta gudana ne a karkashin tsauraran dokokin takaita walwalar jama’a don dakile yaduwar COVID-19, abinda ya sanya mahukunta hana ‘yan kallo halartar filayen wasanni tsawon kwanaki, saboda barkewar annobar da aka samu a sassan birnin Melbourne.

A dai gasar Australian Open din ta 2021 ne kuma mahukuntan Australia suka kori zakaran da ya taba lashe kofin gasar sau tara Novak Djokovic, saboda kin yarda matakin tilasta masa yin allurar rigakafin cutar ta Covid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.