Isa ga babban shafi

Djokovic ya koma Australia bayan janye masa haramcin bizar shekaru 3

Fitaccen dan wasan Tennis a duniya Novak Djokovic na kasar Serbia ya koma Australia, kusan shekara guda bayan da mahukuntan kasar suka kore shi saboda kin amincewar da yayi ya karbi allurar rigakafin cutar Korona.

Novak Djokovica a tsakiyar mukarrabansa, a filin jiragen sama na kasar Australia a ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2022.
Novak Djokovica a tsakiyar mukarrabansa, a filin jiragen sama na kasar Australia a ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2022. REUTERS - LOREN ELLIOTT
Talla

Zakaran gasar Grand Slam har sau 21, ya sauka a kasar ne don gasar Australian Open da za a fara a watan Janairu.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata, dan wasan na Tennis mai kofin Australian Open sau tara, ya samu nasara a kotu wajen soke hukuncin hana shi biza ta tsawon shekaru uku da gwamnatin Australia ta dora masa

A watan Janairun da ya gabata, lokacin da Djokovic ya isa Australia don gasar ta 2022, amma a lokacin annobar Korona ta tsananta, abinda ya sanya dokoki suka bukaci duk wanda ya shiga kasar a yi masa alluran rigakafi - sai dai idan yana da shaidar takardar da ta nuna baya bukatar a yi masa alluar.

Bayan kwanaki 10 Djokovic na jayayya da mahukuntan kasar kan cewa baya bukatar yi masa allurrar, la’akari da cewar bai dade da murmurewa daga cutar ta Covid-19 ba, sai gwamnatin Australian ta soke bizarsa, tare da fayyace ba zai sake komawa kasar ba har sai shekara ta 2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.