Pogba ya tafi yana yaro ya kuma dawo a matsayin zakara - Juventus
Kungiyar Juventus ta bayyana murnar sake kulla yarjejeniya da Paul Pogba, wanda ya sake komawa kungiyar bayan rabuwa da Manchester United.
Wallafawa ranar:
Dan wasan na kasar Faransa wanda ya lashe gasar cin kofin duniya, ya koma kungiyar Juventus dake gasar Seria A kyauta ne sakamakon karewar yarjejeniyarsa da United ba tare da ya sabunta ba.
Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin ta ce, “ Paul ya dawo Turin, ya tafi yana yaro, ya kuma dawo a matsayin cikakken mutum, kuma zakara”
Pogba dai ya taka rawar gani yayin zamansa na Juventus a tsakanin shekarun 2012 zuwa 2016, kafin Manchester United ta saye shi akan Yuro miliyan 105 ciniki mafi tsada a waccan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu