Isa ga babban shafi

Paul Pogba ya yi watsi da tayin Manchester City

Wasu bayanai daga jaridar wasanni ta Gazzetta a Italiya na cewa dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba ya yi watsi da tayin Manchester City a kokarin sayensa don komawa Etihad da taka leda.

Paul Pogba, dan wasan United ta Ingila.
Paul Pogba, dan wasan United ta Ingila. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

A cewar Gazzetta, Manchester City ta amince da dukkanin bukatun Pogba kama daga albashi da alawus alawus da kuma sharuddansa, amma duk da haka dan wasan na Faransa mai shekaru 29 ya yi watsi da tayin saboda tsoron abinda fusatattun magoya baya ka iya yi kan matakin.

Pogba wanda kwantiraginsa zai kare da Man United a karshen wannan kaka na fargabar kada abin da ya faru da Carlos Taves ya faru da shi, lokacin da dan wasan ya sauya sheka daga Manchester United zuwa Manchester City a shekarar 2009 wanda ya rika gamuwa da suka caccaka da kuma barazana daga magoya baya, dalilin da ya dauke tsawon lokacin kafin iya sakin jiki a Etihad.

Akwai dai jita-jitar da ke alakanta Pogba da komawa ko dai Real Madrid ta Spain ko kuma Juventus mai doka Seria A a Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.